T. B. Joshua

T. B. Joshua
Rayuwa
Cikakken suna Temitope Balogun
Haihuwa Arigidi Akoko, 12 ga Yuni, 1963
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Mutuwa Lagos, 5 ga Yuni, 2021
Ƴan uwa
Abokiyar zama Evelyn Joshua
Karatu
Harsuna Turanci
Yarbanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Christian minister (en) Fassara da missionary (en) Fassara
Muhimman ayyuka Synagogue Church Of All Nations (en) Fassara
Imani
Addini Neo-charismatic movement (en) Fassara
T. B. Joshua

Temitope Balogun Joshua (ranar 12 ga watan Yuni shekara 1963 - 5 Yuni 2021) ya kasance fasto mai kwarjini a Najeriya, mai wa'azin telebijin, da kuma taimakon jama'a . Ya kasance shugaba kuma wanda ya kafa majami’ar The Synagogue, Church of All Nations (SCOAN), wannan wata majami’ar kirista wacce ke kula da gidan talabijin na Emmanuel TV daga Legas . Ya kasance ɗaya daga cikin fastocin coci-coci miloniya da suke tuka jirgi masu zaman kansu. Archived 2021-06-06 at the Wayback Machine

T.B Joshua sananne ne sosai a duk faɗin Afirka da Latin Amurka kuma yana da manyan kafofin sada zumunta tare da magoya baya 3,500,000 akan Facebook . Tashar shi ta YouTube, Emmanuel TV, tana da masu amfani da ita a YouTube sama da mutane miliyan 1,000,000 kuma ita ce hidimar kirista ta duniya da aka fi kallo a dandalin kafin a dakatar da ita a 2021. Kafofin yada labarai sun bayyana shi a matsayin "Oprah na Ikklesiyoyin bishara" da kuma "Shahararren Fasto a YouTube".

An ba T.B Joshua lambar yabo iri-iri, musamman ya karbi Jami'in Kungiyar Tarayyar Tarayya (OFR) daga gwamnatin Nijeriya a shekara ta 2008 kuma gidan watsa labarai na Pan-Yoruba Irohin-Odua sun zaɓe shi ɗan Yarbawan na shekaru goma. An kira shi ɗaya daga cikin mutane 50 da suka fi tasiri a Afirka ta mujallar Pan-Afirka The Africa Report da New African Magazine.[1][2][3]

A rahoton jaridar As of 2011Forbes,T.B Joshua ne fasto na uku Mafi arziƙi a Najeriya, daga baya kuma cocin sa ta ƙaryata rahotan10.

  1. "Awo, Soyinka, TB Joshua listed as Yoruba icons". Nigerian Tribune. 20 February 2015. Archived from the original on 28 February 2015.
  2. "The 50 Most Influential Africans". The Africa Report. 30 September 2012.
  3. "2012: 100 Most Influential Africans". New African Magazine. 26 December 2012.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Tubidy